Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU za ta yi zaman ta na karshe a yau Asabar da gobe Lahadi, domin yanke shawara kan lamarin yajin aikin da ta ke neman shiga.
Tuni dai kungiyar ta bayyana cewa, ta fara yanke kauna da gwamnatin Buhari, kuma har idan ta tafi yajin aikin, ba za ta dawo ba, sai lokacin da a ka biya dukkan bukatunsu.
Majalisar zartaswar kungiyar ce ta bayyana cewa, za ta fara zaman kwanaki biyu a jami’ar Legas, Akoka ranar Asabar, domin yanke shawara kan maganar yajin aikin sai baba ta gani.