Firaiministan Pakistan, She]hbaz Sharif ya ce ƙasarsa ta mayar wa da India bikin da ta yi mata.
“Yau mun mayar wa da India bikin da ta yi mana domin ɗaukar fansar jinanen al’ummarmu da ba su ji ba su gani ba.” In ji Shehbaz.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani hari da Pakistan ɗin ta kai yankin Rakesh Gupta wanda ake zargin an yi ne domin kai hari kan fararen hula.
Burtaniya ta ce tana bin tsamin dangatakar tsakanin ƙasashen biyu sau da ƙafa.
Zaman tankiya tsakanin ƙasashen biyu ne dai ya zafafa tun bayan wani hari a watan da ya gabata inda India ke zargin Pakistan da mara wa ƴan ta’adda baya da ke kai hare-hare cikin yankunanta – zargin da Pakistan da musanta.