Shugaban Colombia, Gustavo Petro, ya ce, za a kawo karshen tashe-tashen hankuli a ƙasarsa nan da kwana ɗaya da a ce Majalisar Dinkin Duniya (MDD) za ta halasta amfani da hodar iblis a hukumance a duk fadin duniya.
Da yake jawabi a hukumar samar da zaman lafiya ta MDD a birnin New York, Mista Petro ya ce ribar da ake samu daga fataucin hodar iblis ta haramtacciyar hanya ne ke rura wutar rikicin.
“Abin takaici ne yadda akasarin kasashe ba za su amince da halasta shan irin wadannan kayayyaki ba, sabili da dalilai na siyasa,” in ji shi.
Colombia ce babbar mai samar da hodar iblis a duniya, yayin da Peru da Bolivia ke biye mata baya.
Ba kawai kungiyoyin masu aikata laifuka ne ke rike da hanyoyin safarar miyagun kwayoyin kasar ba, har ma da kungiyoyin ‘yan tawaye, wadanda suka shafe shekara 60 suna yaki da sojojin kasar.


