Wani mutum a Ghana ya rasa ransa bayan da zakuna suka yi tsinke a kansa bayan da ya haura katangar gidan ajiyar namun daji da ke Accra, babban birnin ƙasar.
An hangi mutumin cikin mazaunin zakunan da ƴaƴansu biyu jim kaɗan kafin su afka masa.
Hukumomin gidan ajiyar namun dajin sun killace zakunan kuma tuni aka ɗauke gawar mutumin.
Ƴan sanda na gudanar da bincike domin gano abin da ya sa mutumin ya haura katangar. An yi zargin mutumin ya yi ƙoƙarin sace ɗan zakanya ne kamar yadda wata jarida ta shafin intanet MyJoyOnline ta bayyana.
Hukumomi sun bayyana cewa babu wani zaki da ya ɓace bayan afkuwar lamarin inda kuma suka buƙaci al’umma su kwantar da hankalinsu. In ji BBC.


