Wani likitan dabbobi, Olabode Olawuyi da ke kula da gidan ajiyar namun daji na jami’ar Obafemi Awolowo ya rasa ransa bayan da wani zaki da ya shafe shekara tara yana kula da shi ya yi ajalinsa.
Lamarin dai ya girgiza hukumar jami’ar. Kakakin jami’ar, Abiodun Olanrewaju cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin ya ce marigayin yana wurin kiwon dabbobin domin ba su abinci lokacin da lamarin ya faru.
Olanrewaju ya ce wasu ma’aikatan makarantar sun yi Æ™oÆ™arin kuÉ“utar da shi amma zakin ya riga ya yi masa illa sosai.
“Hukumar gudanarwar makarantar da malamai da daliban jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife a jihar Osun, suna jimamin mutuwar Olabode Olawuyi,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Bayanai na cewa Olabode yana kula da zakin ne tun yana ƙarami.