Da safiyar yau litinin an tsaurara jamiāan tsaro da dama a babban kotun jihar Osun, yayinda kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan ta fara zama.
Gwamna Gboyega Oyetola na kalubalantar sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a ranar 16 ga watan Yuli kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar.
A halin da ake ciki, Oyetola ya bukaci a mayar da zaman kotun zuwa Abuja saboda dalilai na tsaro.
Sai dai shugaban kotun daukaka kara a ranar Jumaāa ya yi watsi da bukatar, inda ya kara da cewa hukumomin tsaro a jihar sun baiwa kotun hadin kai da goyon bayansu wajen inganta tsaron kotun da zamanta.