Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya bayyana cewa dukkan masu neman takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP daga yankin Arewa a shirye suke su bayar da dan takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar ba tare da wata matsala ba.
Bukola ya bayar da wannan tabbacin ne a Bauchi a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da Saraki da Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, wanda kuma mai fatan zama shugaban kasa a jam’iyyar PDP, suka kai ziyarar tuntubar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.
Saraki, wanda ya yi magana da manema labarai a madadin ‘yan takarar shugaban kasa uku, ya ce, sun ga ya zama wajibi a matsayinsu na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar su gana, su yi tunani, domin ganin yadda abubuwa za su daidaita a tsakaninsu. Ya ce: “A yin haka, mun gana, muka tattauna cewa a nan gaba 2023, hadin kai da zaman lafiyar kasar nan da ci gaban kasa ya fi burin mutum daya muhimmanci. Mun kuma hadu domin yin kokari wajen ganin mun yi aiki tare.
Ya kuma ce, “Mun yi imanin cewa mu ukun muna yin aiki tare cikin jituwa, jajircewa da kuzari, za a sami babban fata ga kasar nan.
“Mun yaba da cewa mu ukun mun nuna muradin shugabancin kasar nan, amma kuma mun fahimci cewa, dukkanmu za mu iya, masu cancanta da kuma cancantar shugabancin kasar nan.
“A karshen wannan rana, mutum daya ne kawai zai jagoranci kasar nan a 2023; mun kuma yanke shawarar cewa, za mu yi aiki kafada da kafada ,domin ganin mun fito da hanyar da tsarin yarjejeniya zai zo tsakanin mu uku kan yadda za mu ci gaba da jagorantar kasar nan.”
Tsohon gwamnan na Kwara, ya bukaci daukacin magoya bayan jam’iyyar PDP da su mayar da hankali da hadin kai, domin daukaka jam’iyyar zuwa ga wani matsayi.