Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba ya gana a Legas da shugabannin majalisar wakilai da mataimakansu na jihohi goma sha biyar da jam’iyyar APC ke mulki a kan kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa.
Taron tuntuba, wanda kuma ya samu halartar ‘yan majalisar dokoki na Jihohi da dukkan tsaffin ‘yan majalisar wakilai da suka halarta, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Rt Hon Mudashiru Obasa ne ya shirya taron.
Taken taron shi ne: “Majalisar Dokoki, Canjin Lokaci da Tafiyar Dimokuradiyya ta Najeriya” wanda Tinubu, ya kasance babban bako na musamman.
Mahalarta taron dai sun nuna goyon bayansu ga Tinubu a yunkurinsa na ganin jam’iyyar ta tsayar da shi takarar shugaban kasa.
Gwamnan Jihar, Babajide Sanwo-Olu, ya ce, an nuna karfin jagorancin Tinubu sosai, ganin yadda tsohon Gwamnan Legas ya ke da hangen nesa da kuma ra’ayoyin da suka mayar da yankin karamar hukumar zuwa tattalin arziki mai habaka.