Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya, Sadiq Bello, ya gargadi ‘yan siyasa da su gujewa kawo tashin hankali a zaben 2023.
AIG Sadiq Bello ya yi wannan gargadin ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da kwamishinonin ‘yan sandan Kano da Jigawa a shelkwatar rundunar shiyya daya da ke Kano.
Ya kuma ce”Ya jaddada bukatar ‘yan siyasa da sauran jama’a su guji aikata abubuwan da za su iya haifar da tashin hankali da hargitsi a yayin da za a fara siyasa, muna kira ga jama’a da su kasance masu bin doka da oda, tabbas dimokuradiyya ce, amma akwai muhimman hakkokin al’umma, kuma duk abin da za mu yi ya kamata mu kasance masu bin doka da oda”. Inji Sadiq Bello.