Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta ce jam’iyyar PDP ce ta lashe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihar Gombe.
Jami’ar tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihar ta Gombe, farfesa Maimuna Waziri ta bayyana sakamakon kamar haka:
PDP – 319,123
APC – 146,977
NNPP – 10,520
LP – 26,160
Sauran jam’iyyu – 7,263
Masu zaɓe da aka yi wa rajista – 1,549,243
Masu zaɓen da aka tantance – 542,997
Ƙuri’un da aka kaɗa da kyau – 510,043
Ƙuri’un da suka lalace – 23,735
Yawan waɗanda suka kaɗa ƙuri’a – 533,778