Rahotanni na nuni da cewa, watakil Atiku Abubakar ya rasa tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 2023.
Wani babban jagora a jam’iyyar hamayyar ya ce, zai yi wahala a ce PDP ta sake tsayar da Atiku.
A halin yanzu Gwamnonin PDP masu ci sun sha gaban kowa a jam’iyya, kuma ba sa tare da Atiku.
Wani babba a jam’iyyar hamayya ta PDP, ya ce, da kamar wuya Atiku Abubakar ya rike tutar jam’iyya a zaben shugaban kasa da za ayi a 2023.
A ranar Talata, 8 ga watan Fubrairu 2022, jaridar Vanguard ta rawaito cewa, wannan jigo na jam’iyya ya na cewa gwamnonin PDP su na kara karfi a jam’iyya.
A hirar da aka yi da wannan tsohon gwamna na yankin Arewa maso yamma, ya bayyana cewa gwamnoni ne su ke rike da PDP, kuma sai yadda suka yi.
Ya ce.”Zai yi wahala Atiku ko waninsa ya iya doke wadannan gwamnoni masu ci a zaben fitar da gwani. Ana yi masa hannunka mai sanda, gwamnonin jihohi biyu sun fadawa Atiku gaskiya a ‘yan kwanakin nan, su na nuna masa ya hakura da 2023″. A cewarsa.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed shi ma ya fito gar-da-gar ya na cewa, Atiku Abubakar ya na gaba da su a siyasa, kuma ya cancanta da mulki amma ya tsufa.