Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, gabanin zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa.
A cewar Obi, shi da Jonathan sun yi musayar ra’ayi kan batutuwan da suka shafi kasa a yayin ganawar.
Da yake raba hotunan ziyarar a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, tsohon gwamnan na Anambra ya ci gaba da cewa tattaunawar tasu ta kunshi batutuwan da suka shafi muradun kasa gabanin zaben.
“Kwanan nan na ziyarci babban yayana, H.E. @GEJonathan don yin musayar ra’ayi kan tarin tambayoyi masu muhimmanci na kasa. -PO,” Obi ya saka hoton.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za a fara yakin neman zaben shugaban kasa, da na ‘yan majalisun tarayya ne a ranar 28 ga Satumba, 2022, yayin da na gwamnoni da na majalisun jihohi za a fara a ranar 12 ga Oktoba, 2022.
Kamfen na karshe na jam’iyyun siyasa na takarar shugaban kasa da na majalisar tarayya shi ne da tsakar dare ranar 23 ga Fabrairu, 2023, yayin da na gwamnoni da na majalisun jihohi zai kasance da tsakar dare ranar 9 ga Maris, 2023.