Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabi’u Kwankwaso, a ranar Juma’a, ya ziyarci garin Ilorin na jihar Kwara, domin neman alfarmar Sarkin Ilorin, Alh Ibrahim Sulu-Gambari, domin tabbatar da takararsa ta shugaban kasa.
Kwankwaso ya samu rakiyar dan takarar gwamnan jihar a karkashin jamâiyyar NNPP a jihar, Farfesa Shuaib AbdulRaheem, Alh Buba Galadima da kuma dan takarar Sanatan Kwara ta Arewa a jamâiyyar, Dr Kolo Baba Jiya.
Da yake jawabi a fadar Sarkin jim kadan bayan kammala hidimar Jumaâa tare da Sarkin, Kwakwanso ya ce, ya je Ilorin ne domin neman alfarmar sarauta.
Ya kara da cewa, zai yi amfani da damar ziyarar wajen bude wasu ofisoshin NNPP a Ilorin, babban birnin jihar da sauran sassan jihar.
âMun zo nan ne domin mu girmama ku a matsayinmu na uban gargajiya. Muna godiya da karbo mu da kuma damar gudanar da hidimar Jumaâa tare da ku. Ina kuma mika godiyata ga al’ummar jihar bisa yadda suka nuna mana karimci. Muna adduâar Allah ya karawa Sarkin mu tsawon rai da lafiya,â inji Kwankwaso.
Da yake mayar da martani, Sarkin Ilorin, Alh Ibrahim Sulu-Gambari, ya bayyana Kwankwaso a matsayin gogaggen dan siyasa kuma mai gudanar da mulki.
Ya yi adduâar fatan alheri ga kungiyar Kwankwansiyya, inda ya kara da cewa, âAllah zai ci gaba da yi muku jagora. Na yi matukar farin ciki da na ce kuna maraba.”
Sulu-Gambari ya tabbatar wa dan takarar shugaban kasa na NNPP cewa yana hannun wani mutum mai matukar tasiri a jihar, Farfesa Shuaib AbdulRaheem.
A takaitacciyar jawabinsa, Farfesa AbdulRaheem, wanda ya godewa Sarkin bisa irin karramawar da kungiyar ta NNPP ta yi masa, ya ce Kwankwaso na da dukkan abin da ya kamata domin fitar da alâummar kasar nan daga matsalolin tsaro da tattalin arziki da ke fuskantar ta.