fidelitybank

Zaben 2023: APGA ta fara sayar da fom ɗin takara

Date:

Kwamitin ayyuka na jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), ya kaddamar da shirin gudanar da zabukan 2023 wanda ya fara da sayar da fom din tsayawa takara da kuma nuna sha’awa da aka shirya farawa a ranar Talata mai zuwa.

A cewar wata sanarwa da jam’iyyar APGA ta fitar, kuma aka rabawa manema labarai ranar Juma’a a Abuja, za’a fara siyar da fom na nuna sha’awa da kuma dawo da fom din takara daga ranar 29 ga Maris da 11 ga Afrilu, 2022 Sakatariyar APGA ta kasa, Abuja.

Har ila yau, ta sanar da cewa, za a gudanar da tantance ‘yan takarar majalisar dokokin kasar ne tsakanin 20 da 21 ga Afrilu, 2022, yayin da ake tantance masu neman takarar shugaban kasa da na Gwamna – 22 – 23 ga Afrilu, 2022.

Jam’iyyar ta kuma yi nuni da cewa, ‘yan takarar mata da masu fama da nakasa za su biya kashi 50% na kudaden da aka tanada a sama na duka fom na nuna sha’awa da na takara.

A halin da ake ciki, shugabannin jam’iyyar APGA sun yi jinjina ga tsohon gwamnan jihar Anambra, Cif Willy Obiano bisa ayyukan da ba a saba gani ba a cikin shekaru takwas na gwamnatinsa a jihar.

punch newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp