‘Yan takarar shugaban kasa biyu na kan gaba a zaben 2023 mai zuwa, Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, sun gana a Abuja ranar Litinin a wani bangare na kebantaccen filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja. .
Yayin da Tinubu ke kan hanyarsa ta zuwa garin Jos na jihar Filato domin kaddamar da yakin neman zaben jam’iyyar APC, Atiku yana dawowa daga yakin neman zabensa.
Haka kuma akwai shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyun biyu.
Kwanakin baya, sansanin Atiku ya yi ta zarge-zarge a kan mai rike da tutar jam’iyyar APC wanda sansanin Tinubu ya yi watsi da shi.