Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe a ranar Laraba ta sha alwashin tunkarar duk wani ko wasu mutane da ke da niyyar haddasa tabarbarewar doka da oda a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Mu’azu Mahid Abubakar, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa, ya ce, tuni rundunar ta tsaurara matakan tsaro a kan wasu muhimman kadarori da kayayyakin hukumar zabe ta kasa (INEC) a jihar.
Ya kuma kara da cewa, domin a binciki ayyukan ko masu aikata laifuka a jihar, kwamishinan ‘yan sanda Oqua Etim ya bayar da umarnin tura jami’an ‘yan sanda a kewayen cibiyoyin INEC.
A cewar sa, CP Etim ya kara gargadin ‘yan siyasa da jam’iyyunsu da su guji yin amfani da ‘yan daba wajen gudanar da ayyukan tada zaune tsaye a jihar, kamar yadda ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama za a yi masa da gaske.