Zababben gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda, da safiyar ranar Litinin, ya kai ziyarar ban girma da godiya ga tsohon gwamnan Katsina kuma jigo a jamâiyyar PDP, Ibrahim Shehu Shema, a gidansa na GRA da ke babban birnin jihar.
Mataimakinsa Faruk Jobe ya raka Dikko.
Baya ga Shema da dansa na farko, Yamani Shema, sauran magoya bayan tsohon gwamnan sun yi waje domin tarbar zababben Gwamnan Katsina, mataimakinsa kuma ya hada da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Mashi/Dutsi, Salisu Yusuf Majigiri; Alh. Idi Kwado, Bishir Tanimu, Lawal Dankaba, Rabiu Gambo Bakori, da sauransu.
Shema yayi addu’ar samun nasara ga zababben gwamnan da tawagarsa. Ya kuma tabbatar wa Dikko cewa kofofinsa a bude suke gare shi a kowane lokaci.