Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa, fitacciyar jaruma a Masana’antar Kannywood, Saratu Gidado ta rasu.
Gidan Rediyon Aminci da ke Kano, ya bayar da sanarwa jarumar a yau Talata.
Sanarwar ta ce “Jaruma Saratu Gidado ta rasu, za a yi jana’izarta da karfe 4:00 na yamma a jihar Kano.”
Gabanin ta fara fina-finan hausa shekaru 18 da suka wuce, Saratu Daso malamar makaranta ce. Kuma ta ce aure bai hana ta fim ba. Sannan ta fito a wasu fina-finan turanci