Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ci alwashin zaƙulo mutanen da suka kashe malamin addini Sheikh Ibrahim Musa Albani Kuri.
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin jihar ta ce wasu ɓarayi ne suka kashe malamin ranar Talata da dare yayin da suka shiga gidansa a Tabra da ke birnin Gombe.
“Muna tabbatar wa mazauna Gombe cewa za mu ci gaba da kare dukiya da rayukansu, da kuma zaƙulo waɗanda suka aikata wa malamin wannan mummunan abu,” a cewar gwamnan lokacin da ya halarci jana’izarsa a masallacin Bolari.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Gombe ta ce maharan sun kashe shehin malamin ne yayin da suka yi yunƙurin yi masa fashi.
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Gombe da kuma ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatissunnah (JIBWIS), wanda mamba ne a cikinta.