Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta c,e za ta zafafa yaki da miyagun kwayoyi, inda ta ce lokaci mai wuya yana jiran duk wanda aka kama a yakin.
Sakataren hukumar, Mista Shadrach Haruna, wanda ya wakilci shugaban hukumar, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ya ba da tabbacin cewa NDLEA za ta bi duk wani mai safarar kwayoyi, wanda ya bayyana a matsayin ‘dan kasuwan mutuwa.
Ya yi jawabi ne a wajen taron lacca na shekara-shekara kan shaye-shaye karo na 3 wanda shugabannin majalisar dokokin kasar da kungiyar sa ido kan sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NANDRUM) suka shirya a Abuja inda suka yaba wa hukumar NDLEA kan yaki da matsalar shan miyagun kwayoyi a kasar nan.
Haruna ya amince da kalubalen da ake fuskanta na magance safarar miyagun kwayoyi amma ya ce za a ci gaba da gwabzawa duk da cewa fataucin miyagun kwayoyi na zama sanadin ta’addanci, ‘yan fashi da sauran laifuka.
“Dukkanmu mun san cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi ya kasance kalubale a kasar nan kuma annoba ce ga gidaje da yawa. Mun ga karuwar ‘yan fashi da ta’addanci da duk wasu munanan laifuka da munanan dabi’un al’umma a kasar nan, kuma ana alakanta su da shaye-shayen miyagun kwayoyi. Abin da NDLEA ta kuduri aniyar yi shi ne ‘yantar da Najeriya da ‘yan Najeriya daga matsalolin shaye-shayen miyagun kwayoyi,” inji shi.
Da yake mayar da martani ga tambayoyi kan yadda masu hannu da shuni ke shiga cikin al’umma wajen safarar miyagun kwayoyi, sakataren hukumar ta NDLEA ya bayyana cewa “su ne kungiyoyin da hukumar ta NDLEA ta mayar da hankali wajen kama su a ‘yan kwanakin nan.”
Ya ce: “Shugabannin su ne barayin miyagun kwayoyi da masu safarar miyagun kwayoyi, kuma idan ka bi labarin kwanan nan, za ka gano cewa NDLEA na da barayin kwayoyi kusan ashirin a cikin gidansu.”
Ya bayyana cewa an kama barayin miyagun kwayoyi da dama, an gurfanar da su gaban kuliya tare da daure su tare da kwace musu kadarorin su.