Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jaddada ƙudurin sojojin ƙasar na ci gaba da kai hare-hare zuwa birnin Rafah, duk kuwa da matsin lambar ƙasashen duniya.
A wata hira da ya yi da gidan talbijin na ABC. mista Netanyahu ya ce fiye da Falasɗinawa fararen hula miliyan guda da suka fice daga Rafah da sauran yankunan Gaza, za su samu kariya.
Da aka tambaye shi ko ina wadanna fararen hula za su koma? Sai ya ce Isra’ila na ”aiki kan haka”
Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana cewa Falasɗinawa ba su da wata sauran kariya a Rafah.
Ƙungiyar Tarayar Turai da Amurka da Birtaniya sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da hare-haren.
A nata ɓangare, ƙungiyar Hamas ta ce hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai kwanaki huɗu da suka gabata sun kashe Isra’ilawa biyu da ƙungiyar garkuwa da su tare da jikkata takwas daga ciki.