fidelitybank

Za mu yi wa kowa adalci a shari’ar zaben shugaban kasa – Kotu

Date:

Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafe kan zaɓen shugaban kasa na 2023 ta fara zama a yau Litinin.

Zaman ya fara ne da misalin ƙarfe 9:15 na safe, inda alƙalin da ke jagorantar zaman kotun, mai shari’a Haruna Tsammani ya gabatar da jawabi.

Tsammani ya ce kotun za ta yi wa ƙarar adalci sannan ya gargaɗi lauyoyi da su guje wa yin kalamai na harzuƙawa.

Ya kuma buƙace su da su bai wa kotun haɗin kai domin ganin an kammala shari’ar cikin lokacin da aka ɗiba.

Sauran alƙalan da za su taimaka wajen gudanar da shari’ar sun haɗa da mai shari’a Stephen Adah da Misitura Bolaji-Yusu da Boloukuoromo Moses Ugo da kuma Abbah Mohammed.

Gabanin fara zaman, an jibge jami’an tsaro a kan hanyoyin da suke kai wa zuwa kotun.

Jam’iyyun adawa irin su PDP da LP ne suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar nasarar da ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Sakamakon da INEC ta fitar ya nuna cewa Bola Tinubu na APC ya samu ƙuri’u 8,794,726, sai Atiku Abubuakar na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’a 6,984,520, yayin da Peter Obi na jam’iyyar LP ke biye masu da ƙuri’a 6,101,533.

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp