Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce za ta yi nazari kan gargaɗin da Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar, inda ya yi gargaɗi kan yiwuwar kai hare-hare a ƙasar, musamman babban birnin.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, kwana ɗaya bayan gargadin Amurkan da ma Birtaniya, hukumar ƴan sandan ta ce yin nazarin ya zama wajibi saboda kasancewar rundunar ce kan gaba wajen tabbatar da tsaro na cikin gida.
“Ba za mu yi biris da bayanan leƙen asiri kan barazanar tsaro ba, duk da cewa babu wani abu na tashin hankali da ke faruwa kuma a shirye muke mu yi duk abin da ya dace don shawo kan duk wata barazana.
Bayan haka kuma, rundunar ta ce Babban Sufeton ƴan sanda Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin dukkan kwamishinonin ƴan sanda na jihohin ƙasar su zama cikin shiri tare da sake dabaru don samar da tsaro ga jama’a.
“Rundunar ƴan sanda za ta ci gaba da aiki da sauran hukumomin tsaro don samar da zaman lafiya a Najeriya, musamman babban birnin ƙasar.
Kazalika rundunar ƴan sandan ta sanar da ƙaddamar da aiki na musamman mai taken “Operation Darkin Gaggawa” a shirye-shiryenta na daƙile duk wata barazanar tsaro.


