fidelitybank

Za mu yi karin farashin Burodi a watan Yuli – Kungiya

Date:

Ƙungiyar masu gidajen burodi ta kasa, ta ce, za ta ƙara farashin burodi da kashi 15 cikin ɗari daga ranar 24 ga watan Yuli.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, bayan kammala taron shugabanninta na ƙasa, ƙungiyar ta ‘Association of Master Bakers and Caterers of Nigeria’ ta ce ta ɗauki matakin ne bayan la’akari da nunnukawar farashin kayan aiki.

Sanarwar wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Mansur Umar ta ce tashin farashin ya biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Tarayya ta yi.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a cikin jawabinsa na karɓar mulki.

Lamarin ya haifar da tashin litar man fetur daga kimanin naira 200 zuwa sama da naira 500 a faɗin ƙasar, wani abu da ya haifar da tashin farashin sufuri da kayan masarufi.

Ƙungiyar ta ce abubuwan da take amfani da su wajen gudanar da sana’ar, waɗanda suka haɗa da man fetur, da gas, da fulawa, da suga da sauran su duk sun yi tashin gwauron zabi.

Haka nan ƙungiyar ta koka kan yadda hukumomi daban-daban a ƙasar ke karɓar haraji, kala-kala, wani abu da ke ƙara saka masu gidajen burodin cikin matsi.

Kan haka ne ta ce “An umurci dukkanin shugabannin ƙungiyar na yanki su tabbatar cewa ƴaƴan ƙungiyar sun bi wannan umarni, har sai idan sun samu wani sabon umarnin daga uwar ƙungiyar ta ƙasa.”

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp