fidelitybank

Za mu yi jana’izar Sojoji 17 da aka kashe mana a Delta – Sojoji

Date:

Rundunar sojin ƙasar nan ta sanar da yau 27 ga watan Maris a matsayin ranar da za a yi jana’izar sojoji 17 da aka kashe a garin Okuama da ke jihar Delta.

Rundunar ta ce za a yi jana’izar ne a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ƙarfe 3 na yamma.

Hakan yazo ne ƴan makonni bayan wasu ɓatagari sun kashe wasu daga cikin sojojin da ke aiki ƙarƙashin runduna ta 181 da aka turo domin kwantar da tarzomar da ke tsakanin al’ummar garin Okuama da Okoloba na jihar.

Shugaban ƙasa Bola Tinibu da ƴan Najeriya da dama sun yi allahwadai da kisan sojojin.

Shugaban ƙasa ya umarci rundunar da ta tabbatar cewa waɗanda suka aikata kisan sun fuskanci hukunci. A hoton da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X, sojojin da aka kashe sun haɗa da :

  • Lt Col AH Ali, kwamandan runduna ta 181
  • Manjo SD Shafa
  • Manjo DE Obi
  • Kyaftin U Zakari
  • Staff Sajant Yahaya Saidu
  • Koporal Yahaya Danbaba
  • Koporal Kabiru Bashir
  • Lance Koporal Bulus Haruna
  • Lance Koporal Sole Opeyemi
  • Lance Koporal Bello Anas
  • Lance Koporal Hamman Peter
  • Lance Koporal Ibrahim Abdullahi
  • Private Alhaji Isah
  • Private Clement Francis
  • Private Abubakar Ali
  • Private Ibrahim Adamu
  • Private Adamu Ibrahim

legit news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp