Ƙungiyar ƙwadago ta TUC, ta yi barazanar gudanar da gagarumar zanga-zanga tare da dakatar da al’umura a faɗin ƙasar nan, matuƙar gwamnatin tarayya ba ta soke sabon harajin tsaron intanet da Babban bankin ƙasa ya ɓullo da shi ba.
Shugaban kungiyar Festus Osifo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar yau Laraba.
Hakan na zuwa ne bayan da ƙungiyar ƙwadago ta TUC, ta soki lamirin sabon harajin, wanda ta bayyana a matsayin wani gagarumin nauyi da gwamnati ke ɗora wa talaka.
A ranar Talata ne Babban Bankin Kasa ya fitar da wata sanarwa wadda ke neman a cire harajin kashi 0.5 cikin ɗari kan duk wata hada-hadar tura kuɗi a ƙasar nan suka yi ta intanet.
Ya ce, babu dabara wajen fito da irin wannan haraji daidai lokacin da ƴan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa, sanadiyyar faɗuwar darajar naira da ƙarin farashin man fetur da na lantarki.