Shugaban Hezbollah ya yi gargaɗin cewa ƙungiyar ta Lebanon za ta yi yaƙi ba tare da bin wata ƙa’ida ko shamaki ba, idan har rikici ya kaure tsakaninta da Isra’ila.
Hassan Nasrallah, ya kuma gargaɗi ƙasar Cyprus, da cewa za ta yaba wa aya zaƙinta, idan mamba a ƙungiyar Tarayyar Turan, ta bar sojojin saman Isra’ila su yi amfani da sansanoninta wajen kai hari a Lebanon.
Ya ce, Hezbollah ba ta neman a faɗaɗa yaƙin, amma a shirye take ta ce cas, idan aka ce mata kulle.
Shugaban ya ƙara da cewa babu wani wuri da makamansu ba za su iya kaiwa ba a duk cikin Isra’ila.
Nasrallah na magana ne kwanaki kaɗan bayan ƙungiyar ta fitar da wani bidiyon jirgin leken asiri, da ke nuna wasu muhimman wuraren tsaron soji, na Isra’ila.
Masu sharhi sun ce ta yi hakan ne, don tauna tsakuwa, don aya ta ji tsoro. A cewar