fidelitybank

Za mu tura Sojojin mu zuwa Ukraine – Sweden

Date:

Sweden ta ce ba za ta yi watsi da tura dakarun wanzar da zaman lafiya a Ukraine ba.

Ministar harkokin wajen Sweden, Maria Malmer Stenergard, ta bayyana hakan ta gidan rediyon Sweden.

“Yanzu dole ne mu fara yin shawarwari kan samar da zaman lafiya mai adalci da dorewa wanda ke mutunta dokokin kasa da kasa, da mutunta Ukraine, kuma, da farko, tabbatar da cewa Rasha ba za ta iya janyewa kawai ba, ta sake gina karfinta, da kai hari kan Ukraine ko wata kasa cikin ‘yan shekaru kadan.

“Idan muka samu irin wannan zaman lafiya, muna bukatar mu tabbatar da cewa za a iya kiyaye shi, kuma a lokacin, gwamnatinmu ba ta ware komai,” in ji ta.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da firaministan kasar Birtaniya Keir Starmer ya bayyana shirinsa na aika dakaru zuwa Ukraine a wani bangare na matakan wanzar da zaman lafiya.

A jiya litinin, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya isa kasar Saudiyya gabanin tattaunawar da ake sa ran zai yi da jami’an Rasha da nufin kawo karshen yakin da Moscow ta shafe kusan shekaru uku ana gwabzawa a Ukraine.

A halin da ake ciki, shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana aniyarsa ta ganawa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.

An yi imanin ganawar Trump da Putin na da nufin kawo karshen yakin Ukraine.

Shugaban na Amurka wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya ce yana bakin kokarinsa wajen ganin an samu zaman lafiya.

Ya bayyana cewa ya yi imani da Putin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky na son dakatar da fada.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp