Mai tsaron ragar Equatorial Guinea, Jesús Owono, ya sha alwashin dakatar da dan wasan Najeriya Victor Osimhen lokacin da kungiyoyin biyu suka fafata a gasar cin kofin kasashen Afrika (AFCON) da za a yi ranar Lahadi.
Owono ya kuma yi alkawarin dakatar da abokan wasan Osimhen Samuel Chukwueze, Kelechi Iheanacho, Ademola Lookman, Moses Simon, Terem Moffi da Ahmed Musa.
Dukkan kungiyoyin biyu suna rukunin A ne tare da kasar Ivory Coast mai masaukin baki.
Osimhen shi ne ya fi zura kwallo a raga a gasar neman gurbin shiga gasar AFCON ta 2023 da kwallaye 10.
Dan wasan Napoli ya wuce Sadio Mane na Senegal.
Da yake magana a taron manema labarai na gabanin wasan, Owono ya ce, “Zan yi iya kokarina wajen dakatar da Victor Osimhen da sauran ‘yan wasan Super Eagles domin samun sakamako mai kyau a wasan farko.”
Lokacin da za a take wasan shine 3:00 na yamma.