Tawagar Likitoci daga ƙungiyar agaji ta ‘International Committee of the Red Cross (ICRC) za ta tallafa wa likitocin asibitin Maidugiri wajen yi wa mutanen – da harin ƙunar baƙin wake a Gwoza – magani.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce tawagar ƙwararrun likitocin nata za ta yi aiki da likitin asibitin koyarwa na birnin Maiduguri wajen ceto rayukan mutanen da harin ya yi musu mummunar illa.
Mutane da dama ne suka samu munanan raunuka a lokacin harin da wasu ‘yan ƙunar baƙin wake suka kai garin Gwoza a ƙarshen mako.
An kai mutum 41 da suka jikkata zuwa asibitin na Maiduguri, da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ranarkun Asabar da Lahadi domin ba su kulawar gaggawa.
Ƙungiyar ICRC ta kuma bayar da tallafin magunguna da wasu kayyaki ga asibitin domin taimaka wa ɓangaren kula da masu buƙatar kulawar gaggawa.
Mataimakiyar shugaban tawagar ƙungiyar da suka je Maiduguri, Diana Japaridze ta ce halin da marasa lafiyar ke ciki a asibitin ”abin tayar da hankali ne”.
“Muna kira da babbar murya cewa a yaƙi dole a kare fararen hula musamman mata da ƙananan yara, kuma asibiti wuri ne na ceton rai, ba wurin salwantar da rai ba.”
”Hari kan mai uwa da wabi kan fararen hula, abu ne da ya saɓa wa dokokin duniya, haka ma cibiyoyin kula da lafiya da ma’aikata, su ma dole ne su samu kariya, ba a kai musu hari ba”, in ji ta.
A ranar Asabar ne wasu mata huɗu suka tayar da boma-bomai a wurare daban-daban a Gwoza lokacin da ake tsaka da bikin aure.
Lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 32 tare da jikkata gommai, kamar yadda mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana.