Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce ta wani bidiyo da ke yawo na zargin tsare wani sojan ruwa mai suna Seaman Abbas Haruna tsawon shekaru shida.
Hedikwatar rundunar tsaron ta Najeriya a wata sanarwa mai sa hannun kakainta, Birgediya Janar Tukur Gusau ta “muna bai wa al’ummar Najeriya tabbacin cewa rundunar tsaron Najeriya a shirye take ta samar da adalci da daidaito bisa dokokin Æ™asa.
Shari’a a kotun soji duk da dai yana É—aukar lokaci amma tana tabbatar da adalci kamar yadda tsarin aikin soji ya tanada.”
Sanarwar ta ƙara da cewa a wani martani ga wannan zargi, babban hafsan sojin ƙasar, Janar Christopher Musa ya ba da umarnin fara binciken gaggawa domin gano haƙiƙanin abin da ya faru kuma za a sanar da ƴan ƙasa sakamakon binciken.
“Muna bai wa Æ´an Najeriya tabbacin cewa rundunar tsaron Najeriya za ta tabbatar da an gudanar da bincike kan al’amarin ba tare da É“ata lokaci ba kuma za a gudanar da binciken a faifai.” In ji sanarwar.
A makon da ya gabata ne dai mai É—akin Seaman Abbas ta je gidan rediyo na Human Rights Radio da aka fi sani da Brekete Family a Abuja, inda ta bayyana irin halin da maigidan nata yake ciki tsawon shekaru shida a hannun rundunar sojin saman Najeriya.,