Gwamnatin tarayya ta ce, ta karye farashin shinkafa wadda ta tanada da za a sayar a sassan kasar da nufin samar da sauki ga ƴan kasa.
A kasuwa dai ana sayar da shinkafar ne kusan N80,000, ɗaya daga cikin dalilan da suka sa wasu ƴan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga domin nuna fushinsu da tsadar rayuwa.
Amma Gwamnatin tarayya ta ce ta karya farashin shinkafar zuwa N40,000 kan duk buhu daya 50kg, kamar yadda ministan yada labarai na kasar Muhammad Idris ya shaida wa BBC.
Ya ce tuni an ware wuraren da za a sayar da shinkafar a sassan jihohin Najeriya. Sai dai gwamnatin ba ta bayyana lokacin da za ta fara sayar da shinkafar mai sauƙin kuɗi ba.
Amma a cewar ministan, karya farashin na zuwa bayan gwamnatin tarayya ta bayar da tirelar shinkafa 20 ga duk jihohin ƙasar domin raba wa ƴan Najeriya.
“Da farko an ba gwamnoni shinkafa su raba wa masu ƙaramin ƙarfi kyauta kuma yanzu gwamnati ta tanadi shinkafa da za ta sayar da rahusa domin samar da sauƙi ga ƴan Najeriya,” in ji ministan.
Ya ce shinkafar da za a sayar a farashi mai rahusa ba wadda gwamnatin tarayya ta raba wa gwamnonin jihohi ba ce.
Shinkafa na ɗaya daga cikin abincin da ake ci a Najeriya, kuma farashinta a kasuwa kusan ya gagari aljihun wasu ƴan ƙasar.
Ministan ya ce gwamnati ta lura da tsadar shinkafar a kasuwa, shi ne ya sa ta ɗauki matakin samar da ita a farashi mai rahusa domin ƴan ƙasa su amfana
Kuma a cewarsa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.
“Idan aka ci gaba da kawo matakai irin waɗannan, sannu a hankali abubuwa za su yi sauƙi.”


