Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin maƙala wa dabbobi ɗan-kunnne mai amfani da fasahar zamani
Ɗan-kunnen zai taimaka ne wajen sanin tarihi da bayanan da suka shafi dabba da kuma bin labinta a duk inda take.
Gwamnatin ta ƙaddamar da shirin ne tare da haɗin-gwiwa da ƙungiyoyin makiyaya da nufin magance matsalar satar shanu da inganta kasuwancinsu a gida da wajen Najeriya.
Gwamnatin ta bayyana cewa, lokaci ya yi da ya kamata a cusa fasahar zamani a cikin harkar kiwo ta yadda za ta ci gajiyar cigaban a da ake samu.
Shirin, a cewar gwamnati zai taimaka wajen magance matsalolin da makiyaya ke fama da su kasar, musamman satar shanu, da rashin rumbun bayani a kan dabbobi da zai taimaka wajen fito da tsare-tsare na inganta harkar kiwo fataucin dabbobi ko nama da sauran abubuwan da suke samarwa.