Burtaniya ta ce, ta zura ido kan ‘yan siyasa da jam’iyyunsu, jami’an tsaro da duk wani mutum da zai haifar ko ingiza rikici ta shafuka sada zumunta gabannin babban zaɓe da ke tafe a 2023 a ƙasar.
Jakadiyar Burtaniya a Najeriya, Catriona Laing ce ta sanar da hakan lokacin ganawa da kwamitin gudanarwa ta harkokin zaɓe na PDP a Abuja.
Ms Laing ta ce zaɓen 2023 na da muhimmanci sosai ga Afirka da duniya baki ɗaya, don haka dole ido na kan Najeriya kuma Burtaniya za ta zura ido sosai a kan ƙasar.
Ta kuma ce Burtaniya ta damu matuƙa kan abubuwan da suka faru na baya-bayanan, ciki harda rikice-rikice 52 da ke da alaƙa da zaɓe a jihohi 22, ciki harda harin da aka kai wa tawagar PDP a Borno.
Ta ce Burtaniya ba za ta goyi-bayan kowacce jam’iyyar siyasa ba, domin tana da burin ganin kowane ɗan kasa ya samu damar zaɓin abin da yake gani shi ne cancanta a gareshi.
Jami’ar ta kuma shaida cewa suna ta tattaunawa da masu ruwa da tsaki, ciki harda Inec, da kungiyoyin fararan-hula da ‘yan siyasa domin tabbatar da sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali.