Kungiyar Take It Back Movement, wata kungiya ce mai fafutukar kare hakkin bil adama a bayan zanga-zangar EndBadGovernance da aka kammala, ta yi barazanar sake gudanar da zanga-zangar a fadin kasar game da kudirin doka mai cike da takaddama kan taken kasar.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa a yanzu haka akwai wani kudirin doka da ke neman hukunta ‘yan Najeriya da suka ki rera taken kasar a zauren majalisar wakilai.
Kudirin dokar wanda kakakin majalisar Tajudeen Abbas ke daukar nauyinsa, na neman a ci tarar Naira miliyan 5 ko shekaru 10 a gidan yari ko kuma duka biyun ga duk wanda ya lalata alamomin kasa, ya ki karanta taken kasa da kuma yin alkawari.
Da take mayar da martani, kungiyar Take It Back a wata sanarwa da ta fitar a ranar Larabar da ta gabata ta yi watsi da kudurin dokar, inda ta ce hakan na barazana ga ‘yancin ‘yan Najeriya.
Sanarwar wacce kodinetan kungiyar na kasa, Juwon Sanyaolu ya sanya wa hannu ta ce “ya kamata a yi watsi da kudirin ba a amince da shi ya zama doka ba, a’a, ya kamata gwamnati ta mayar da kokarinsu wajen magance matsalolin da ke haifar da rashin jituwa da rigingimu a kasarmu. “.
Sun yi barazanar gudanar da zanga-zanga a fadin kasar idan har dokar ta zama doka duk da nuna fushin da jama’a suka yi.
Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa, “A matsayin kungiyar masu goyon bayan jama’a da suka sadaukar da kansu don tabbatar da adalci da ci gaba, mun lura da yadda jama’a ke mayar da martani ga kudirin, yayin da ‘yan kasar ke nuna rashin jin dadinsu.
“Mun dauki wannan doka a matsayin wani yunkuri na tauye ‘yancin ‘yan Najeriya, kuma muna alfahari da tsayawa tare da jama’a wajen kara zage damtse wajen yin Allah wadai da wannan kudiri na rashin adalci.
“A cikin hadin kai da al’ummar Najeriya, mun yi tir da wannan doka ta danniya, kuma mun sha alwashin kare ‘yancin da tsarin mulki ya ba ‘yan Najeriya.
“Ba za mu daina komai ba don kare duk abin da ya rage na ‘yancin dimokiradiyya a matsayinmu na ‘yan Najeriya, ciki har da tara ‘yan Najeriya a kan tituna idan ba a janye wannan doka mai tsanani ba.”