fidelitybank

Za mu sake duba Jarrabawar UTME ta shekarar – JAMB

Date:

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta ce, za ta sake duba Jarrabawar UTME ta shekarar 2025, bayan korafe-korafe da yawa daga jama’a kan matsalolin fasaha da tambayoyi da ba su cika ba, da kuma sakamakon ƙaramin maki ba kamar yadda aka saba ba.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Fabian Benjamin ya fitar, JAMB ta bayyana cewa ta karɓi “ƙorafe-ƙorafe da ba su saba ba” tun bayan fitar da sakamakon jarrabawar a ranar Jumma’ar da ta gabata.

Sanarwar ta ce wannan ƙoƙorafe-ƙorafen ne ya saka hukumar ta yanke shawarar yin bincike cikin gaggawa saɓanin yadda aka saba yi a baya watanni bayan kammala jarrabawar.

An haɗa ƙwararru daga fannin kimiyyar kwamfuta da masu kimanta jarrabawa da shugabannin jami’o’i don taimakawa a aikin.

JAMB ta tabbatar da cewa idan aka gano wata matsala a tsarin, za ta ɗauki matakan gyara da suka dace nan take.

A halin yanzu kuma, rahotanni na nuna cewa dubban waanda suka rubuta jarabawa na shirin shigar ƙara a kotu bisa zargin rashin daidaito a gudanar da jarabawar.

www.najnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...
X whatsapp