Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta soki Shugaban Rasha Vladimir Putin inda ta ce ya dawo da yaƙi nahiyar Turai.
Ta bayyana haka ne a yayin da take jawabi a birnina Brussels na kasar Belgium.
Ta sanar da cewa za a saka takunkumai masu ƙarfi nan ba da jimawa ba domin raunata tattalin arziƙin Rasha da kuma ci gabanta.