Gwamnatin jihar Legas ta ce, za ta sanya takunkumi kan masu magungunan gargajiyan da ke harkokinsu a jihar.
Hukumomi a jihar sun sanya wa’adin ranar 6 ga watan Fabrairu mai kamawa, cewa idan har masu maganin suka ƙi yin rijistar wuraren sana’oinsu da hukumar kula da magungunan gargajiya ta jihar, za su fuskanci takunkumi.
Hakan dai wani mataki ne na kawar da masu magungunan gargajiya na bogi a jihar, a cewar jami’ai.
Magatakardar hukumar kula da magungunan gargajiya ta jihar, Babatunde Aderemi, ya ce yin rajistar zai taimaka wajen tantance masu gaunguna na gaskiya da kuma na jabu.
Haka kuma ya kƙara da cewa duk wasu masu magungunan gargajiyan da dangoginsu da suka kasa sabunta lasisinsu zuwa wannan lokaci, za a cire sunayensu a rajistar.
A cewarsa za a yi hakan ne kamar yadda dokar harkokin lafiya ta jihar ta tanada.
Wasu masu magungunan gargajiya da ke jihar sun yi maraba da matakin, inda suka bayyana buƙatar a yi tantancewar ba tare da wata manufa ba.
Dubban ƴan Najeriya ne ke amfani da magungunan gargajiya saboda dalilan da suka hada da talauci da ƙarancin ƙananan asibitoci a kusa, lamarin da ke jefa rayukansu cikin haɗari.