fidelitybank

Za mu rufe Jami’o’in Najeriya – ASUU

Date:

Ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta cika yarjejeniyar da suka shiga a shekarar 2009 ko ta tsunduma yajin aiki.

Shugaban ASUU, Chris Piwuna ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma’a a Abuja.

Ya nanata buƙatar da ke akwai na gwamnatin ta cika yarjejeniyar da alƙawuran da ta ɗauka domin magance matsalolin da jami’o’in ƙasar ke fuskanta.

Piwuna ya ce har yanzu akwai wasu muhimman batutuwa guda tara da ba a daddale su ba a yarjejeniyar da suka shiga.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa daga cikin abubuwan da suka rage akwai albashin malaman da ba a biya ba lokacin da suke yajin aiki na shekarar 2022 da wasu alawus ɗinsu da ake riƙe saboda IPPIS da sauransu.

Ya ce duk da alƙawarin da gwamnati ta yi na zuba naira biliyan 150 domin gudanar da jami’o’in ƙasar da inganta alawus na malaman, har yanzu ba su gani a ƙasa ba.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp