Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN, a ranar Juma’a ta yi barazanar rufe gidajen man da ke sayar da fiye da farashin da aka amince.
Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar IPMAN, Alhaji Bashir Dan Malam wanda aka rabawa manema labarai a Kano ta kuma sha alwashin hukunta duk wani dan kasuwa da ya sayar da kayan sama da farashin famfo da aka amince da shi.
Alhaji Bashir Dan Malam ya bayyana bukatar masu zaman kansu da ‘yan kasuwa su sayar da kayan a kan farashi mai inganci domin ba sa biyan karin kudi ga hukumar NNPC kafin samun rabon.
Sai dai ya ja kunnen ‘yan kasuwar da su yi taka-tsan-tsan da wasu mutane da ke da dabi’ar amfani da gidajen man da aka yi musu rajista wajen karbar kaso daga Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ba bisa ka’ida ba.
Shugaban na IPMAN ya ce shawarar ta zama wajibi ne biyo bayan korafe-korafe da hukumar ta NNPC ta yi na cewa wasu mutanen da ba su da sana’ar sayar da man fetur suna da dabi’ar karbar kason mai daga kamfanin ba bisa ka’ida ba ta hanyar gabatar da sunayen wasu gidajen man da aka yi wa rajista.
Danmalam ya ce an dauki matakin bayar da gargadin ne a wata ganawa da aka yi tsakanin shugabannin hukumar ta NNPC da kuma shugabannin IPMAN.
A cewarsa, kamfanin ya yi barazanar soke lasisin siyan kaso mai tsoka na duk wani dan kasuwa da aka samu ya bar irin wadannan mutane su yi amfani da gidan man da aka yi wa rajista don samun rabo daga bisani su sayar da kayayyakin ga wasu.
Don haka shugaban na IPMAN ya gargadi masu aikata wannan aika-aika da su daina yin hakan domin duk wanda aka kama za a kai rahoto ga jami’an tsaro domin daukar matakin da ya dace.
Ya kuma kara da cewa hukumar gudanarwar NNPC da ta IPMAN ba za su nade hannayensu ba, su bar irin wannan ta’asa ta ci gaba da cutar da masu sayar da man fetur na gaskiya a kasar nan.
Dan-Malam a cikin sanarwar ya yabawa mahukuntan NNPC da ke karkashin jagorancin Mele Kyari bisa tabbatar da wadatar kayayyakin.