Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya mai zaman kanta ta sanar da cewa, za a rage farashin Man Fetur (Premium Motor Spirit) da Naira 50 idan an dauke man Dangote kai tsaye.
Shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Maigandi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Maigandi ya bayyana cewa matatar man Dangote ta amince ta sayar da man fetur ga mambobinta akan farashin Naira 940 da kuma Naira 990 kan kowacce lita na depots da manyan motoci.
A cewarsa, dangane da farashin man fetur na Dangote, ‘yan kungiyar IPMAN wadanda a halin yanzu suke sayar da kayan a tsakanin Naira 1,150 zuwa Naira 1,200 kan kowace lita za su rage farashin da Naira 50 ya danganta da wurin.
“A halin yanzu, an ba mu tsari guda biyu kan yadda za mu sayi man fetur daga matatar.
“Akwai wanda za mu iya loda tasoshin mu kai zuwa rumfunanmu daban-daban akan farashin Naira 940 kan kowace lita. Sannan na depots, akan farashin N990 akan kowace lita.
“Misali, farashin yanzu a Maiduguri ya kai Naira 1,200 kowace lita. Don haka da wadannan sauye-sauyen da ake samu a yanzu, ana iya ragewa zuwa N1,150, wato rage N50. To N1,150 kenan. Yana iya ma yana ƙasa da hakan,” in ji shi.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Litinin din da ta gabata ne kungiyar IPMAN ta sanar da cewa matatar man Dangote ta amince da sayar da man fetur ga mambobinta kai tsaye, lamarin da ya kawo karshen kamfanin man fetur na Najeriya, wanda shi ne ke siyan man fetur din Dangote.
Wannan ci gaban ya biyo bayan sanarwar da matatar man Dangote ta bayyana cewa ana sayar da man fetur din ta akan naira 960 da kuma naira 990 akan kowacce lita na jiragen ruwa da manyan motoci.