Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris, ya ce gwamnatinsa za ta raba manyan motoci 200 ɗauke da abinci dangin hatsi don rage wa al’ummar jihar raɗaɗin tsadar rayuwa da suke ciki.
Cikin wata sanarwa gwamnatin jihar ta fitar a shafinta na X, ta ce ta sayi hatsin ne da nufin tallafa wa rayuwar al’ummar jihar.
”Gwamnatinmu ta sayi na’urorin sola don samar da wutar lantarki, da kuma injunan samar da ruwan sha masu amfani da man gas na CNG don inganta noma da samar da abinci”, in ji sanarwar.
A wani labarin na daban kuma gwamnan ya sanar da bai wa kungiyar ‘yan sintiri ta Vigilanti tallafin naira miliyan 50 don inganta ayyukanta na samar da tsaro a jihar.
Gwamnan ya kuma alkawarta sayen motoci da sauran kayan aiki ga kungiyar.
Gwamnan ya ce ingantuwar tsaro a yankunan Zuru da Yauri ya sa manoman yankunan sun koma gonakinsu, lamarin da gwamnan ya ce ya taimaka wajen ƙaruwar samar da abinci a yankunan.