fidelitybank

Za mu miƙa DCP Abba Kyari ƙasar Amurka ya girbi abun da ya shuka – Gwamnati

Date:

Gwamnatin Najeriya ta amince da buƙatar Amurka ta miƙa mata ɗan sanda DCP Abba Kyari wanda ake zargi da hannu wajen aikata zambar fiye da dala miliyan ɗaya ta intarnet tare da Ramon Abass.

Ofishin Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan, ranar Alhamis bayan ministan ya gabatar wa Babbar Kotun Tarayya a Abuja buƙatar miƙa ɗan sandan wanda tuni aka dakatar da shi.

Antoni janar ɗin ya ce, ya nemi a kai Abba Kyari Amurka ne, bayan buƙatar da ƙasar ta gabatar masa, inda ya yi amfani da dokar miƙa wanda ake zargi da laifi ƙasashen ƙetare ta Extradition Act a gaban kotun.

Sai dai babu ƙarin bayani a yanzu game da abin da zai faru da sauran zarge-zargen da hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi, NDLEA, take yi masa na safarar hodar ibilis idan aka kai shi Amurka.

Tun a 2021 ne Amurka ta zargi DCP Kyari da mu’amala da Ramon Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi wanda kuma tuni yake tsare a ƙasar, da damfarar wasu kamfanoni fiye da dala miliyan ɗaya.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp