Babban kamfain mai na kasa NNPCL, ya bayyana aniyarsa ta mayar da matatun man fetur na ƙasar da ke Warri da na Kaduna hannun ‘yan kasuwa.
Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa shafin na X, NNPCL ya ce ya ɗauki matakin ne domin ci gaba da gudanarwa tare da kula da matatun biyu.
An kafa matatar Warri – wadda ke jihar Delta a yankin kudu maso kudancin ƙasar – a shekarar 1978.
Matatar na da ƙarfin da za ta iya tace gangar mai 125,000 a kowace rana, sannan tana iya tace wasu sinadaran masu alaƙa da albarkun man fetur.
An kafa matatar ne da nufin samar da mai ga yankunan kudanci da kudu maso yammcin ƙasar.
A ɗaya ɓangaren kuma an ƙaddamar da matatar mai ta Kaduna – da ke arewacin ƙasar – a shekarar 1980, domin samar da man fetur ga yankin arewacin Najeriya.
Matatar na da ƙarfin tace gangar 110,000 a kowace rana.