Shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi ya ce ƙasarsa ta shirya tattaunawar sulhu.
Mista Raisi ya ce “idan kai mai yawan surutu ne da ɓaɓatu, to mu ba haka muke ba, kuma ba mu bar teburin sulhu ba.”
A lokaci guda kuma, ya ce “yaren da ake amfani da shi domin tunzura Iran ba zai karya mana gwiwa ba.”
Ebrahim Raisi ya kwatanta manufofin harkokin wajen ƙasar da na lokacin Hassan Rouhani yana cewa lokacin da mutum zai nemi cinikayya kan makamanmu, kuma a yi shi yadda ya ga dama.”
“Jiya, wasu mutane sun ce, ba za mu iya rubuta taken mutuwar Isra’ila ba da makamai, wanda zai janyo zaman ɗarɗar ga makiyanmu, amma yau makaman rokarmu za su iya sauka a tsakiyar birnin maƙiyanmu domin su fahinci laifukan da suke yi da kuma kisan kiyashin da suke yi.”