Shugaban kasa Bola Tinubu, ya ba da umarnin sake dawo da tsarin ciyar da ɗaliban makaranta domin magance ƙalubalen rashin zuwan yara makaranta.
Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne ya dakatar da tsarin bayan shafe shekaru ana tafiyar da shi.
Sai dai a yanzu shugaba Tinubu ya ba da umarnin a farfaɗo da tsarin saboda zai taimaka wajen magance matsalolin da suka shafi ilimi.
Ya ce idan ba a magance matsalar ba, zai yi matuƙar wahala a iya rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka a wani taron yini ɗaya da aka yi.
Ministan ya ce an yi taron ne domin samar da hanyoyin aiwatar da dukkanin tsare-tsaren da za su magance duk wasu ƙalubale da kuma yadda hukumomi daban-daban za su taimaka wajen rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.


