Rundunar ƴan sanda ta jihar Kano ta ce, ta ɗauki matakin ladabtarwa a kan jami’anta biyar da aka gani a faifan bidiyo suna taimaka wa wani ɗan siyasa wajen shirya jama’a domin karɓar kuɗi a gidan gwamnatin jihar.
Sanarwar da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a madadin kwamishinan ƴan sandan jihar Kano a ranar Talata, 19 ga Agusta, 2025.
Sanarwar ta bayyana cewa bincike ya gano lamarin ya faru ne bayan wani taro a ɗakin taro na Coronation Hall da ke gidan gwamnati na Kano a ranar 10 ga Yuli, 2025, kuma bai da wata alaka da zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar a ranar 16 ga Agusta, 2025.
Rundunar ta ce jami’an sun aikata rashin kwarewa yayin da aka tura su aikin tsaro, kuma yanzu haka an fara ɗaukar matakan ladabtarwa a kansu domin tabbatar da tsari da kare mutuncin rundunar.
Haka kuma, an jaddada cewa rundunar ƴan sanda za ta ci gaba da jajircewa wajen bin ƙa’idoji da kiyaye amana da ɗabi’a domin samun amincewar jama’a.