Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce yana sa ran za su karɓe ikon tsaro a Gaza da zaran sun kammala kakaɓe Hamas.
A wani jawabi da ya gabatar ta talabiji, Netanyahu ya ce matakin zai kasance na dindindin.
Sanan Ya ce da Isra’ila ke kula da harkokin tsaro a Gaza, da yanzu ba a samu yaɗuwar ta’addanci ba.
Netanyahu ya ƙara da cewa za a cigaba da ɗan tsahirtawa kamar na sa’a guda zuwa ɗan lokaci domin bada damar shigar da kayan agaji Gaza.
Netanyahu ya kuma jadadda cewa babu wani batun tsagaita wuta har sai Hamas ta saki mutanensu da take rike da su, yana mai cewa batun ya dakatar ganganci ne da ka iya lalata kokarinsu.