Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya ce gwamnatinsa za ta kawo ƙarshen zaman dukkan sojojin ƙasar waje a ƙasar tasa da ke Afirka ta Yamma.
Yayin wani jawabi na sabuwar shekara da ya yi ta talabijin ranar Talata, Faye ya ce ya bai wa ministan tsaro umarnin tsara sabon daftarin tsaro da kuma ƙawance, ciki har da kawo ƙarshen zaman dakarun ƙasashen waje a ƙarshen 2025.
A ranar 28 ga watan Nuwamba, Faye ya sanar cewa zaman sojojin Faransa a Senegal bai dace da ‘yancin ƙasar na cin gashin kanta ba.
Sanarwar da Faye ya bayar ta zo daidai lokacin da ƙasashen Afirka da dama suka kori dakarun Faransa kuma suka koma ƙawance da Rasha.
Faransa na da dakaru kusan 350 a Senegal.