fidelitybank

Za mu koma fagen daga idan Hamas ba ta saki ‘yan kasar mu ba – Isra’ila

Date:

Isra’ila ta ce za ta koma yaƙi tare da fatali da yarjejeniyar tsagaita wuta, matsawar Hamas ba ta saki Isra’ilawan da ke take garkuwa da su ba a ranar Asabar.

Firaministan Isra’ila Benjami Netanyahu bai fayyace ko yana nufin duka mutanen da Hamas din ke garkuwa da su, ko kuma ukun da aka tsara saki a ranar ƙarƙashin yarjejeniyar.

Netanyahu ya umarci dakarun ƙasarsu su taro a ciki da kewayen Gaza, yayin da Hamas ke cewa Isra’ila ce ”ta janyo duk abin da ya faru na jinkirin da aka samu”.

Ƙungiyar ta ce ta jinkirta sakin mutanen da aka tsara za ta saki a ƙarshen makon da muke ciki, bayan da ta zargi Isra’ila da saɓa wa sharuɗan yarjejeniyar, sai dai ta ce har yanzu tana son ci gaba da aiki da yarjejeniyar.

An fahimci cewa ƙasashen Larabawa na matsa wa ƙungiyar lamba kan komawa aiki da yarjejeniyar.

Tun da farko shugaban Amurka, Donald Trump ya yi gargaɗin cewa idan ba a saki Isra’ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza ba ”za a yi duk bala’in da za a yi”, matakin da Netanyahu ya yi maraba da shi a ranar Talata.

Kawo yanzu Falasɗinawa da suka koma Gaza byan fara aiki da yarjejeniyar, na cikin fargaba da tashin hankali.

thisday newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp